Yan Tawayen Kasar Sudan Ta Kudu Sun Kai Hari Cikin Kasar Kenya
Majiyar rundunar 'yan sandan Kenya ta sanar da cewa: 'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan al'ummar garin Lokichogia da ke shiyar arewa maso yammacin kasar Kenya.
Majiyar rundunar 'yan sandan Kenya a yankin Turkana a shiyar arewa maso yammacin kasar ta bayyana cewa: 'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun kai harin wuce gona da iri kan al'ummar garin Lokichogia a yau Asabar, inda suka kashe mutane akalla 6 tare da jikkata wasu adadi masu yawa.
Kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta tabbatar da kai harin tare da hanzarta kai dauki ta hanyar daukan wadanda suka samu raunuka a jirgin sama mai saukar ungulu zuwa asibitin garin Eldoret da ke yammacin kasar ta Kenya domin kula da lafiyarsu.
Yankin Turkana da na Lokichogia suna daga cikin yankunan da suke makobtaka da kasar Sudan ta Kudu, kuma ana yawan samun bullar fadar da makami a tsakanin al'ummar yankunan kan sabani dangane da mallakar gonakin noma da albarkatun karkashin kasa.