Kenya: 'Yan hamayyar Siyasa Suna Ci Gaba da Yin Zanga-zanga.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24949-kenya_'yan_hamayyar_siyasa_suna_ci_gaba_da_yin_zanga_zanga.
Zanga-zangar tana ci gaba ne duk da cewa babban dan hamayya Raila Odinga, ya janye da sake karawa da shugaba Uhuru Kenyatta a zabe anan gaba.
(last modified 2018-08-22T11:30:50+00:00 )
Oct 15, 2017 12:25 UTC
  • Kenya: 'Yan hamayyar Siyasa Suna Ci Gaba da Yin Zanga-zanga.

Zanga-zangar tana ci gaba ne duk da cewa babban dan hamayya Raila Odinga, ya janye da sake karawa da shugaba Uhuru Kenyatta a zabe anan gaba.

Radiyon Faransa na kasa da kasa, ya ce; Kasar ta Kenya ta zama filin dagar yin taho mu gama a tsakanin jami'an tsaro da kuma 'yan hamayyar siyasa. Abinda 'yan hamayyar suke so shi ne a dakatar da zaben shugaban kasa na 26 ga watan Oktoba.

Odinga ya janye ne saboda an ki amincewa da bukatun da ya gabatar na yi wa hukumar zaben kasar kwaskwarima.

A ranar 18 ga watan Augusta ne aka yi zaben shugaban kasa a Kenya wanda aka bayyana Uhuru Kenyatta a amtsayin wanda ya lashe shi. Sai dai 'yan hamayyar sun nuna kin amincewa da sakamakon,abinda ya jawo taho mu gama a tsakaninsu da jami'an tsaro da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Bayan da kotun kolin kasar ta rusa zaben, ta bukaci da a a gabatar da wani sabon zaben a ranar 26 ga watan Oktoba.