Somaliya: Harin Ta'addanci Ya Kashe Mutane 40
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24951-somaliya_harin_ta'addanci_ya_kashe_mutane_40
'Yan sandan kasar ta Somaliya sun ce mutane sun mutu ne saboda tarwatsewar wata mota da aka makare da bama-bamai a babban birnin kasar Magadishu.
(last modified 2018-08-22T11:30:50+00:00 )
Oct 15, 2017 12:25 UTC
  • Somaliya: Harin Ta'addanci Ya Kashe Mutane 40

'Yan sandan kasar ta Somaliya sun ce mutane sun mutu ne saboda tarwatsewar wata mota da aka makare da bama-bamai a babban birnin kasar Magadishu.

Harin shi ne mafi girma da ya faru a cikin kasar ta Somaliya  a baya-bayan nan kamar yadda majiyar 'yan sandan ta tabbatar.

Wannan harin na faru ne a daidai lokacin da kasar take ci gaba da kokawa da matsalolin rashin tsaro,siyasa da tattalin arziki. 

A cikin shekara daya, kasar ta Somaliya ta sami sauyi a siyasance, inda aka gudanar da zaben shugaban kasa bayan lokaci mai tsawo.

Kungiyar 'yan ta'adda ta al-shabab ita ce barazana mafi girma ta tsawo da kasar take fuskanta, haka nan wasu kasashen makwabta.