Bukatar Kungiyar AU na gyara a kwamitin Tsaro na MDD
Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Bukaci da gudanar da gyara a kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya
Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na kasar China ya habarta cewa a yayin bude taron ta na shekara shekara da ya gudana jiya Assabar a birnin Adis Ababa, kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci da a gudanar da gagarimin gyara a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Dunya kama daga manbobin kwamitin da kuma tsari da zai yi daidai da bukatun kasashen Duniya
Kungiyar Ta ce kwamitin tsaron MDD yana jinkiri sosai wajen daukan mataki a kan rikicin kasa da kasa.
Shugaban Kungiyar mai barin Gwado Robet Mugabet ya tabbatar da cewa a taron da kungiyar da gudanar a Suizilland sun bukaci da a baiwa kungiyar AU Kujeru biyu na dindin din a kwamitin, amma har yanzu babu wata amsa da kwamitin ya bayar.
Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya ce Africa za ta janye daga Majalisar dinkin duniya idan har a ka ci a gaba da watsi da bukatun nahiyar.
A jiya Assabar ne dai kungiyar AU ta fara zaman ta na shekara-shekara karo na 26 , wanda kuma za a kawo karshen sa a yau Lahadi.
Taron da aka bude jiya ya fi meda hankali ne kan bunkasar Nahiyar, yaki da take Hakin bil-adama, kare hakin Mata da kuma yaki da ta'addanci.
har ila yau kungiyar ta zabi Idrisa Deby shugaban kasar Tchadi a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar har na tsahon shekara guda.