Buhari Ya Soki Gwamnonin Jihohi Kan Rashin Biyan Albashin Ma'aikata
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25005-buhari_ya_soki_gwamnonin_jihohi_kan_rashin_biyan_albashin_ma'aikata
Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Nigeria ya soki gwamnonin jihohi kan rashin biyan albashin ma'akatansu duk tare da tallafin da ya bayar don hakan.
(last modified 2018-08-22T07:00:51+00:00 )
Oct 17, 2017 15:34 UTC
  • Buhari Ya Soki Gwamnonin Jihohi Kan Rashin Biyan Albashin Ma'aikata

Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Nigeria ya soki gwamnonin jihohi kan rashin biyan albashin ma'akatansu duk tare da tallafin da ya bayar don hakan.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Talata a lokacinda yake ganawa da wakilan majalisar gwamnoni wadanda suka kawo masa ziyarar aiki a fadar shugaban kasa a Abuja. 

Shugaba Buhari, ta bakin kakakin fadar shugaban kasa Mr Femi Adesina ya fadawa shugaban majalisar gwamnonin Abdul aziz Abubkara Yari na jihar Zamfara kan cewa ya damu da labaran da yake samu na cewa har yanzun akwai ma'aikatan da ba'a biya su albashi na watanni. 

Tare da shugaban majalisar gwamnonin dai akwai gwamnonin jihar Ondo, Kebbi, Bauchi, Jigawa, Kwara da kuma Akwa-Ibon da kuma mataimakon gwamnan jihar Ebonyi da suka ziyarci shugaban a yau. 

A nashi Bangaren shugaban majalisar gwamnonin Alhaji AbdulAziz yari ya fadawa shugaban kan cewa gwamnonin sun gaji basussuka masu yawa a lokacin da suka kama aiki, kuma sun yi amfani da kudaden ga gwamnatin tarayyar ta bayar kamar yadda ya dace.