Hukumar Kwastam A Nigeria Ta Kwace Motoci 3000 Daga Dillalansu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25016-hukumar_kwastam_a_nigeria_ta_kwace_motoci_3000_daga_dillalansu
Hukumar kwastam a tarayyar Nigeria ta bayyana halaccin kwace motoci kimani 3000 da tayi daga hannun dillalan motoci a duk fadin kasar a tsakanin watan Janairu na wannan shekara zuwa yanzu.
(last modified 2018-08-22T07:00:51+00:00 )
Oct 18, 2017 08:27 UTC
  • Hukumar Kwastam A Nigeria Ta Kwace Motoci 3000 Daga Dillalansu

Hukumar kwastam a tarayyar Nigeria ta bayyana halaccin kwace motoci kimani 3000 da tayi daga hannun dillalan motoci a duk fadin kasar a tsakanin watan Janairu na wannan shekara zuwa yanzu.

Jami'n hulda da jama'a na hukumar ta kwastam Mr Joseph Attah ya fadawa jaradar Daily Trusrt ta Nigeria kan cewa kwace motocin da jami'an hukumar suka yi daga hannun dillalan motoci a duk fadin kasar ya yi daidai da doka ta 147 ta hukumar wato (CEMA). Attah ya kara da cewa gwamnatin kasar  ta hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar na kasa sai dai ta ruwa. Don haka sun kwace dukkan motocin da aka shigo da su kasar ta hanyoyin da ba su dace ba ne.

Jami'in ya kara da cewa jami'an hukumar sun kwace motocin da aka shigo da su ba bisa ka'ida ba, kuma duk wanda bai yi laifi ba kada ya damu , hukumar ba za ta cutar da shi ba. Hukumar tana aiwatar da abin da gwamnatin tarayyar kasar take so ne.