Kenya: Daya Daga Cikin Mambobin Hukumar Zabe Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25034-kenya_daya_daga_cikin_mambobin_hukumar_zabe_ya_yi_murabus
mamban da ya yi murabus mai suna Roselyn Akombe, daya ne daga cikin mambobi 8 da hukumar take da su.
(last modified 2018-08-22T11:30:51+00:00 )
Oct 19, 2017 06:25 UTC
  • Kenya: Daya Daga Cikin Mambobin Hukumar Zabe Ya Yi Murabus

mamban da ya yi murabus mai suna Roselyn Akombe, daya ne daga cikin mambobi 8 da hukumar take da su.

A wata sanarwa da Roselyn Akombe ya fitar ya ce a halin da ake ciki a yanzu, hukumar zaben ba za ta iya gudanar da gamsasshen zabe mai tsabta ba a ranar 26 ga watan nan na Oktoba, don haka ba ya son ya taka rawa a ciki.

Roselyn Akombe ya ci gaba da cewa; Idan rayuwar mutane tana fuskantar hatsari, to wajibi ne a ja da baya.

Zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 1 ga watan Satumba ya jawo cece kuce, da rikici a kasar ta Kenya. Raila Odinga wanda ya yi takara da shugaba Uhuru Kenyatta, ya ki amincewa da sakamakon zaben.

 A karshe kuma kotun kolin kasar ta soke zaben tare da yin kira da a sake  shirya wani zaben.