Somaliya Ta Sha Alwashin Yaki Da Al-Shabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25042-somaliya_ta_sha_alwashin_yaki_da_al_shabab
Shugaban kasar Somaliya, Mohamed Abdullahi Mohamed, ya sha alwashin ci gaba da yaki da kungiyar Al'shabab, bayan mummunan harin da kungiyar ta kai wanda ya yi ajalin a kalla mutum 300.
(last modified 2018-08-22T11:30:51+00:00 )
Oct 19, 2017 17:37 UTC
  • Somaliya Ta Sha Alwashin Yaki Da Al-Shabab

Shugaban kasar Somaliya, Mohamed Abdullahi Mohamed, ya sha alwashin ci gaba da yaki da kungiyar Al'shabab, bayan mummunan harin da kungiyar ta kai wanda ya yi ajalin a kalla mutum 300.

Shugaban ya bayyana hakan ne jiya a gaban dandazon jama'ar kasar dake halartar taron juyayin wadanda harin mafi muni a tarihin kasar ya rusa dasu.

Harin wanda aka kai da wata babbar mota a ranar Asabar data gabata a Mogadisho babban birnin kasar ya dai fusata jama'ar kasar ta Somaliya ba kadan ba.

Shugaba Abdullah ya ce harinb na ranar Asabar ya nuna cewa ba mu yi abun azo a gani ba wajen kawo karshen kungiyar ta Al-shabab, don haka ya dace muyi hadin kai mu kuma jajirce don ganin bayan wannan kungiya.

Babu dai karin bayyani kan irin matakan da gwamnatin Somaliyar da ta kama iko watanni takwas da suka gabata za ta dauka na murkushe kungiyar.