Hare-Haren Ta'addanci A Birnin Maiduguri Ya Jawo Asarar Rayuka Akalla 13
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25131-hare_haren_ta'addanci_a_birnin_maiduguri_ya_jawo_asarar_rayuka_akalla_13
Akalla mutane 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hare-haren kunar bakin wake da aka kai a tashar Muna da ke cikin birnin Maiduguri na Jihar Borno a tarayyar Nigeria.
(last modified 2018-08-22T07:00:53+00:00 )
Oct 23, 2017 02:58 UTC
  • Hare-Haren Ta'addanci A Birnin Maiduguri Ya Jawo Asarar Rayuka Akalla 13

Akalla mutane 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hare-haren kunar bakin wake da aka kai a tashar Muna da ke cikin birnin Maiduguri na Jihar Borno a tarayyar Nigeria.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto cewa hare-haren sun auku ne da misalin karfe 8.50 na dare a cikin tashar motoci ta Muna a cikin karamar hukumar lere na cikin birnin Maiduguri.

Wani daga cikin mayakan sa kai na CJTF ya bayyana cewa daya daga cikin yan kunar bakin waken ya tarwatsa kansa a cikin tashar inda ya kashe mutane 13 sannan wasu 6 suka ji  raunuka.

Wata majiya ta fadawa wakilin jaridar Dailytrust ta wayar tarho kan cewa hari na biyu ya auku ne a cikin sansanin yan gudun hijira inda ya raunata mutane 10 sannan ya kashe kansa. 

Wani jami'an bada agaji ya ce mai yiwuwa yawan wadanda suka mutu ya karu, kuma aikin ceto a garejin Muna a lokacin yana da hatsari ga ma'aikatan ceton don haka ba zasu iya sanin yawan wadanda abin ya shafa ba sai yau Litinin da safe.