Tsoffin Yan Sandan Biafra Sun Yi Maraba Da Biyansu Kudaden Ritaya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25173-tsoffin_yan_sandan_biafra_sun_yi_maraba_da_biyansu_kudaden_ritaya
Tsoffin 'yan sandan Biafra a gabancin tarayyar Nigeria sun yi maraba da biyansu kudaden fansho bayan shekaru 47 da kawo karshen yakin basasa a yankin.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Oct 25, 2017 15:32 UTC
  • Tsoffin Yan Sandan Biafra Sun Yi Maraba Da Biyansu Kudaden Ritaya

Tsoffin 'yan sandan Biafra a gabancin tarayyar Nigeria sun yi maraba da biyansu kudaden fansho bayan shekaru 47 da kawo karshen yakin basasa a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Nigeria NAN ya bayyana cewa tsoffin yansandan Biafara wadanda aka yi masu afuwa a shekara ta 2000 sannan shugaban Buhari ya amince a biyasu kudaden ritayarsu sun yi murna da wannan matakin .

Babban sakatarin hukumar pensho Mrs Sharon Ikeazor ta fadawa tsoffin yansanda wadanda suka halarci taron bude shirin biyansu kudaden ritayansu a ranar Jumma'a kan cewa shugaban Buhari zai kawo karshen duk wahalhalun da suke ciki.

A hiran da NAN ta yi da wasu tsoffin yansandan Biafara sun nuna jin dadinsu da wannan matakin, sun kuma godewa shugaban kasar da tausayin da ya yi masu. 

A makonnnin da suka gabata be shugaban Buhari ya amince a biya tsoffin yansandan biafara kudaden Penshon bayan da gwamnatin Obasanjo ta yi masu afwa a shekeata ta 2000.