Oct 27, 2017 12:20 UTC
  • Ziyarar Ministan Harkokin Wajen Iran A Nijar

A ci gaba da ran gadin da ya ke a wasu kasashen Afrika, ministan harkokin waje na Jamhuriya musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya isa birnin Yamai na Jamhuriya Nijar.

A ziyara ta sa a Nijar, Mista Zarif ya gana da mayan jami'an gwamnatin kasar da suka hada da firayi ministan kasar Birji Rafiji da kuma shugaba Isufu Mahamadu.

Babban jigon ziyarar dai shi ne karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu da tattauna batutuwan da suka shafi yankin da kuma na kasa da kasa.

A yayin ziyara ministocin harkokin waje na kasashen biyu sun jagoranci bude wani babban taron kasuwanci tsakanin Iran da Nijar.

Wannan ziyara ta Zarif na zuwa ne bayan wacce ya kai a kasashen Afrika ta Kudu da kuma Uganda.

 

Tags