Najeriya : Reshen (IS) A Yammacin Afrika Ya Dau Alhakin Harin Yobe
Kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ta dauki alhakin harin da ya yi sanadin mutuwar sojojin Najeriya a kalla 15 a wani kauye dake jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar.
A wata sanarwa da ta fitar ta Intanet da harshen larabci, kungiyar ta (IS) ta ce mayakanta ne suka kai harin a sansanin sojin dake jihar Yobe, kuma sun yi awon gaba da makamai da kuma wasu motocin soji.
Reshen kungiyar ta IS a yammcin AFrika (SWAP) a takaice da Abu Mus'ab al-Barnawi ke jagoranta ne ya kai harin a cewar sanarwar.
Harin dai an kai shi ne a ranar Talata data gabata a kauyen Sasawa dake nisan kilomita 45 daga Damaturu babban birnin jihar Yobe, shi ne kuma irinsa na uku da kaiwa sojojin kasar a kasa da makwanni biyu.
Tun da farko dai an sanar da mutuwar sojoji takwas a harin, aman a jiya Juma'a wata majiya soji ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa adadin sojojin da suka gamu da ajalinsu a harin ya kai 15, bayan da aka gano sauren gawawakin sojojin ciki har da wani ofisa.
Majiyar ta kara da cewa har yanzu ana cigiyar wasu sojoji da ba'a san halin da suke ciki ba kawo yanzu.