Jami'an Tsaron Tunusiya Sun Kame Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Kasar
Rundunar sojin Tunusiya ta sanar da kame wasu gungun 'yan ta'adda da suke shirye-shiryen kai hare-haren wuce gona da iri kan 'yan yawon shakatawa a lardunan kasar biyu.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Tunusiya ta fitar da sanarwar cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kame wasu gungun 'yan ta'adda da suke shirye-shiryen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan 'yan yawon shakatawa a lardunan Monastir da Sidi Bouzid a jiya Juma'a, kuma bayan gudanar da bincike kansu sun yi furuci da alakarsu da kungiyar ta'addanci ta Da'ish.
Tun bayan bullar guguwar canji da ta yi awungaba da gwamnatin Zainul-Abideen bin Ali a shekara ta 2011, ayyukan ta'addanci suka kunno kai a Tunusiya lamarin da ya janyo matsalar koma baya a harkar gudanar da yawon shakatawa a kasar tare da bullar matsalolin tattalin arziki da rashin aikin yi a kasar.