Mutane Akalla 17 Suka Mutu Sanadiyyar Tashin Boma-Bomai Biyu A Magadishu
Motoci biyu makare da boma bomai sun yi bindiga sun kuma kashe akalla mutane 17 a birnin Magadishu babban birnin kasar Somalia a jiya Asabar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya ce wannan shi ne tashin bom na farko tun bayan mafi munin tashin bom da aka yi makonni da suka gabata. Tuni dai kungiyar Alshabab ta dauki alhakin tayar da boma boman.
Labarin ya kara da cewa a wannan karon yan ta'adda sun tuka mota guda suka burmata a cikin wani otel kusa da fadarb shugaban kasa, sannan wasu yan ta'addan suka kutsa cikin otel din sannan suka tada bom a cikin mota ta biyu. Wani jami'in yansanda mai suna Ali Nur ya shaidawa reuters cewa mafi yawan mutanen da suka rasa rayukansu yansanda ne.
Labarin ya ce daya daga cikin tsoffin yan majalisar dokokin kasar ta Somalia na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a hare haren na jiya Asabar. Daraktan kamfanin Amin Amblances Abdulkadir Abdulrahim ya fada wa Reuters cewa motocinsa sun kai mutane 17 asbiti dauke da raunuka masu tsanani..