An Kori Kwamandan 'Yan Sanda Da Shugaban Hukumar Leken Asirin Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25243-an_kori_kwamandan_'yan_sanda_da_shugaban_hukumar_leken_asirin_somaliya
Gwamnatin kasar Somaliya ta sallami babban sufeto janar na 'yan sanda da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar daga mukamansu biyo bayan hare-haren ta'addancin da aka kai birnin Mogadishu, babban birnin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:55+00:00 )
Oct 30, 2017 02:20 UTC
  • An Kori Kwamandan 'Yan Sanda Da Shugaban Hukumar Leken Asirin Somaliya

Gwamnatin kasar Somaliya ta sallami babban sufeto janar na 'yan sanda da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar daga mukamansu biyo bayan hare-haren ta'addancin da aka kai birnin Mogadishu, babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayyana cewar biyo bayan bukatar da ministan tsaron kasar Mohamed Abu Bakr Islou ya gabatar wa gwamnatin sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai birnin Mogadishun a ranar Asabar din da ta gabata, gwamnatin ta amince da korar babban sufeto janar na 'yan sanda da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar daga mukamansu.

Rahotanni daga kasar sun ce kimanin mutane 23 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 30 kuma suka sami raunuka sakamakon harin ta'addancin da kungiyar Al-Shabab ta kai birnin na Mogadishu. Kafin hakan ma a wani harin ta'addancin da aka kai birnin na Mogadishu a ranar 14 ga watan Oktoban nan, sama da mutane 350 ne suka mutu baya ga wasu da suka sami raunuka.

Sama da shekaru 30 kenan kasar Somaliyan take cikin mawuyacin hali na tsaro da ayyukan ta'addanci sakamakon rashin wata takamammiyar gwamnatin a kasar.