Najeriya : Buhari Ya Kori Babashir Daga Gwamnatinsa
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kori wasu mayan jami'an gwamnatinsa biyu da suka hada da sakataren gwamnati Babachir Lawal da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA Ambasada Ayo Oke.
An dai sallami jami'an ne bisa zarginsu da hannu a wata badakallar cin hanci da karbar rashawa kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar cikin wata sanarwa a yau Litini.
A watan Afrilu da ya gabata ne aka dakatar da aikin jami'an biyu, inda shi Babashir ake zarginsa da hannu a saba ka'idojin bada kwangila karkashin shirin gwamnati na raya yankin arewa maso gabas wanda Boko Haram ta daidaita.
Sanarwar ta ce tuni shugaba Buharin ya maye gurbin Babashir Lawal da Muhammad Boss.
Shi kuwa Ayo Oke ana zargin da karkata kudade da yawansu ya kai dala miliyan 43 na hukumar ta NIA, bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gano wasu kudaden a wani gidansa dake Lagas.
'Yan kasar da dama dai sun jima suna jiran su ga irin matakin da shugaban kasar zai dauka kan mutanen biyu, bayan kafa wani kwamiti da zai binciki zarge-zargen.