Najeriya Ta Amince Biyan 'Yan Biafra Diyya
Shekaru kusan hamsin bayan kawo karshen yakin Biafra (1967-1970), gwamnatin Najeriya ta amince biyan wadanda yakin Biafra ya shafa diyya.
Gwamnatin Najeriya ta amince da hakan ne bisa hukuncin da kotun raya tattalin arzikin kasashen yankin yammacin Afirka (ECOWAS) ta yanke.
Najeriyar ta ce za ta biya diyya ta Naira Bilyan hamsin ga wadanda yakin ya shafa, a jihohi 11 a yankin kudu da kudu maso gabashin kasar da kuma wasu yankunan da yakin na tsawan shekaru uku ya shafa.
Ko baya ga hakan gwamnatin Abuja ta ce za ta biya naira bilyan 38 domin tsarkake duk yankin daga nakiyoyin da ababe masu fashewa da aka dana a lokutan yakin, tare da gudanar da wasu ayyukan na gina makarantu da kotuna da kuma coci-coci.
Wasu bayanai daga kamfanin dilancin labaren AFP, sun ce kimanin abubuwa masu fashewa 17,000 aka lalata cikin 'yan shekarun baya bayan nan a yankin, aman akwai wasu 1,317 da har yanzu suke a yankin.