Buhari Ya Rantsar Da Sabon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya
(last modified Wed, 01 Nov 2017 18:18:58 GMT )
Nov 01, 2017 18:18 UTC
  • Buhari Ya Rantsar Da Sabon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin tarayyar kasar Boss Mustapha a yau din nan Laraba inda ya fara aikinsa a matsayin sabon sakataren gwamnatin.

Rahotanni sun ce shugaba Buhari ya rantsar da Mr. Boss Mustapha din ne  jim kadan kafin zaman mako-mako da majalisar ministocin kasar take gudanarwa a birnin Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriyan, taron da ya sami halartar gwamnan jihar Adamawa Mohammed Jibrilla.

Sabon sakataren dai zai maye gurbin tsohon sakataren gwamnatin Tarayyar ne Babachir Lawan wanda shugaba Buharin ya tube shi a ranar Litinin din da ta gabata saboda zargin cin hanci da rashawa da ake masa.

'Yan Nijeriya dai suna ci gaba da maraba da korar tsohon sakataren gwamnatin da aka yi suna masu kiran da a gurfanar da shi a gaban kotun tare da shugaban hukumar leken asiri na NIA  Ayo Oke da shugaban ya kore su tare da Mr. Babachir Lawal din shi ma saboda zargin satar kudaden gwamnatin.