EFCC Ta Gayyaci Tsohon Daraktan NIA Da Matarsa Don Amsa Tambayoyi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25293-efcc_ta_gayyaci_tsohon_daraktan_nia_da_matarsa_don_amsa_tambayoyi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta gayyaci tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Nijeriyar (NIA), Ambasada Ayodele Oke da matarsa don amsa tambayoyi dangane da dala miliyan 43 da aka samu a wani gida a Lagos mallakinsu.
(last modified 2018-08-22T07:00:56+00:00 )
Nov 03, 2017 02:22 UTC
  • EFCC Ta Gayyaci Tsohon Daraktan NIA Da Matarsa Don Amsa Tambayoyi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta gayyaci tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Nijeriyar (NIA), Ambasada Ayodele Oke da matarsa don amsa tambayoyi dangane da dala miliyan 43 da aka samu a wani gida a Lagos mallakinsu.

Kafafen watsa labaran Nijeriyan dai sun bayyana cewar a jiya ne dai hukumar ta EFCC ta bukaci Ambassador Oke da matarsa tasa tare da wasu mutane na daban-daban da ake zargi cikin wannan badakalar da su kai kansu ofishin hukumar da ke Lagos don ci gaba da yi musu tambayoyi kan wannan batun.

Wannan gayyatar dai ta zo 'yan kwanaki ne bayan da shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya kori Mista Oke daga mukamin nasa bayan da rahoton da wani kwamitin bincike da shugaba Buharin ya kafa karkashin jagorancin mataimakinsa Yemi Osinbanjo ya same Mista Oke da hannu cikin wannan badakalar.

A farko-farkon wannan shekarar ne dai jami'an hukumar EFCC din suka gano wadannan makudan kudade a wani gida dake garin na Lagos mallakin iyalan Mr. Oke din da ake zargin an same su ne ta barauniyar hanyar, lamarin da ya sanya shugaba Buharin dakatar da shi daga aiki da kuma kafa kwamitin bincike.