Ethiopia Ta Tura Dubban Sojoji Zuwa Somaliya Don Fada Da Al-Shabab
Gwamnatin kasar Ethiopia ta tura dubban sojojinta zuwa ga kasar Somaliya a kokarin da kasashen yankin suke yi na fada da kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab da take ci gaba da zama babbar barazana ga zaman lafiya kasashen yankin.
Rahotanni sun jiyo mutanen garin Dolow da ke kan iyakan kasashen biyu suna fadin cewa sun ga kimanin motocin soji 30 dauke da sojoji tare da manyan makamai suna shiga kasar Somaliyan.
Ana ganin tura sojojin dai a matsayin cika alkawarin da gwamnatin Ethiopian ta yi ne na kara tura sojojinta don karfafa sabon shirin da aka shigo da shi na fada da kungiyar ta Al-Shabab da nufin ganin kawo karshenta a yankin. A kwanakin baya ne dai shugaban kasar Somaliyan Mohamed Abdullahi Mohamed ya bukaci taimakon kasashen Uganda, Ethiopia da Djibouti da suke makwabtaka da kasar wajen fada da kungiyar ta'addancin.
Kungiyar al-Shabab din ta kashe dubun dubatan sojoji da fararen hulan kasar Somaliyan da ma na makwabta sakamakon hare-haren ta'addanci da take kai wa kasashen.