Zambiya : Edgar Ya Ja Kunnan Alkalai Kan Yunkurin Hana Shi Tazarce
Shugaba Edgar Lungu, na Zambiya ya ja kunnan alkalan kasarsa akan yunkurin hana shi yin tazarce a wani sabon wa'adi a zaben shugabancin kasar na 2021.
Mista Lungu ya fada a gaban magoya bayansa cewa'' ya gayawa alkalan da ya kira da abokansa da kada su jefa kasar a cikin rudani akan wannan batun''.
Shugaba Lungu wanda ke shugabancin wannan kasa ta Zambiya tun 2015 ya sha nanata aniyarsa ta yin tazarce a wani sabon wa'adi a 2021, lamarin da ya hadassa zazzafar muhawara a kasar.
Kundin tsarin mulkin kasar Zambiya dai ya tanadi wa'adin mulki biyu na shekaru biyar-biyar ga shugaban kasa.
An dai zabi Edgar Lungu a shekara 2015 bayan mutuwar shugaba Michel Sata shekaru biyu kafin karshen wa'adin mulkinsa, an kuma sake zabensa a zaben shugabancin kasar na 2016 mai cike da rudani.
Shid ai shugaba Lungu na cewa yana da damar sake tsayawa takara don bai cika wa'adi biyu ba cikaku, batun da 'yan adawa suka ce basu lamunta da shi ba.