Rikici Yana Ci Gaba Lashe Rayukan Jama'a A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
(last modified Sat, 04 Nov 2017 19:31:02 GMT )
Nov 04, 2017 19:31 UTC
  • Rikici Yana Ci Gaba Lashe Rayukan Jama'a A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Kungiyar Likitoci Maras Kan Iyaka ta Doctor's Without Borders da ke gudanar da ayyukan jin kai a duniya ta bada labarin cewa: Rikici tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya yana ci gaba da lashe rayukan mutane.

A bayanin da kungiyar ta Doctor's Without Borders ta fitar ta jaddada tsananin damuwarta kan yadda rikici da tashe-tashen hankula suke ci gaba da habaka a yankin Batangafo da ke arewacin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, inda a cikin kwanaki ukun da suka gabata dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a yankin ya lashe rayukan mutane akalla 16 tare da kona gidaje masu yawa.

Rahotonni sun bayyana cewa: Rikicin ya kunno kai ne tsakanin kungiyar 'yan dabar kiristoci ta Anti-Balaka da kungiyar Central African Patriotic Movement "MPC" a takaice wadda take wani bangare ne na babban kungiyar 'yan tawayen Seleka ta mabiya addinin Musulunci a kasar a kokarin da 'yan dabar Anti-Balaka suka yi na mamaye yankunan musulmi a yankin na Batangafo da ke arewacin kasar.