Shugaban Tarayyar Afirka Na Ziyarar Aiki A Kasar Sudan
Nov 06, 2017 08:47 UTC
Shugaban na tarayyar Afirka Musa Faki Muhammad wanda ya gana da jami'an gwamnatin kasar Sudan ya yi kira da a dawo da zaman lafiya da sulhu a yankin Darfur.
Tun a 2014 ne gwamnatin kasar Sudan ta yi kira da a janye dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasa da kasa da suke a yankin Darfur. gwamnatin ta Sudan tana ganin cewa an sami zaman lafiya mai dorewa a cikin yankin Darfur don haka babu bukatar ci gaba da zaman dakarun tabbatar da zaman lafiya a cikinsa.
Sai dai a lokaci guda an ci gaba da samun tashe-tashen hankula a cikin yankin na Darfur daga lokaci zuwa lokaci.
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da janye dakarun nata na zaman lafiya daga yankin na Darfur.
Tags