Sudan: Gwamnati Na Shirin Rufe Sansanonin 'Yan Gudun Hijira A Yankin Darfur.
Shugaban kasar ta Sudan Umar Bashir ne ya sanar da cewa; Tunda an kawo karshen yaki a yankin, lokacin rufe sansanin 'yan gudun hijira ya yi a Darfur.
Shugaban na kasar Sudan wanda yake jawabi a jiya litinin ya ci gaba da cewa: " Abu mai muhimmanci da ke gabanmu a yanzu shi ne rufe sansanonin 'yan gudun hijira, saboda bamu da bukatar wasu 'yan gudun hijirar."
Umar Hassan Al-Bashiri ya ci gaba da cewa; Wajibi ne ga dukkanin 'yan gudun hijirar da su koma garuruwansu domin za mu tabbatar da tsaronsu da kuma samar musu da bukatun yau da kullum."
Shugaban na Sudan ya kuma zargi kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa da amfani da sunan 'yan gudun hijira domin samo kudade daga kasashen duniya, domin amfanin kansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce; Da akwai mutane miliyan uku da suke da bukatuwa da agaji. A tsakaninsu da akwai mutane miliyan daya da 600,000 da suke rayuwa a cikin sansanonin 'yan gudun hijira 60.