D R Congo : Amurka Ta Bukaci Kabila Ya Bar Iko Bayan Zabe
Amurka ta bukaci shugaba Joseph Kabila na Jamhuriya Demukuraddiyar Kongo da ya bar iko bayan zaben kasar dake tafe.
Wannan dai ya biyo bayan da aka tsaida ranar babban zaben kasar na watan Disamba na shekara mai zuwa ta 2018.
A cikin sanarwar data fitar gwamnatin Amurka ta ofishin jakadancinta dake Kinshasa babban birnin Jamhuriya Demukuraddiyar Kongo ta yaba da fiatar da jadawalin zaben kasar dake tafe.
A jadawalin zaben da aka fitar a ranar Lahadi data gabata, an shirya gudanar da zaben shugaban kasa a Kongo a ranar 23 ga watan Disamba 2018.
A ranar 20 ga watan Disamba shekara data gabata ne ta 2016 wa'adin karshe na mulkin shugaba J. Kabila, wanda ke shugabancin wannan kasa ta DRC tun shekara 2001 ya kawo karshe.
Saidai duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa sake tsayawa takara, aman kotun kasar ta bashi damar ya ci gaba da mulki har sai an zabi sabon shugaba.