Najeriya : Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2018
Nov 07, 2017 13:48 UTC
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gabatar wa da majalisar dokokin kasar, kasafin kudin shekara 2018 da ya kai naira tiriliyan 8.6
Kasafin kudin na shekara mai zuwa ya zarta na bana da kashi 16% .
A jawabinsa ga majalisar dokokin kasar yayin gabatar da kasafin yau Talata, Shugaba Buhari ya ce gwamantinsa tana tsammanin za ta samu kimanin naira tiriliyan 2.442 daga albarkatun mai.
Shugaba Buhari ya ce gwamnati za ta kashe naira biliyon 300 kan gyara hanyoyi a fadin kasar da kuma ware naira biliyon 8.9 domin tashar samar da wutar lantarki ta Mabila .
Tags