Shugabar Liberiya Ta Ce Demokradiyyar Kasar Na Fuskantar Barazana
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25372-shugabar_liberiya_ta_ce_demokradiyyar_kasar_na_fuskantar_barazana
Shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf ta bayyana cewar tsarin demokradiyyar kasar na fuskantar matsin lamba da kuma barazana, kwana guda bayan da kotun koli ta kasar ta dakatar da gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar saboda zargin an tafka magudi.
(last modified 2018-08-22T07:00:57+00:00 )
Nov 08, 2017 07:50 UTC
  • Shugabar Liberiya Ta Ce Demokradiyyar Kasar Na Fuskantar Barazana

Shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf ta bayyana cewar tsarin demokradiyyar kasar na fuskantar matsin lamba da kuma barazana, kwana guda bayan da kotun koli ta kasar ta dakatar da gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar saboda zargin an tafka magudi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar shugabar ta bayyana hakan ne a wani jawabi da ta yi wa al'ummar kasar ta gidan radiyon kasar inda ta ce: Tsarin demokradiyyar mu na fuskantar barazana. Haka nan mutumcin kasarmu na fuskantar barazana, kamar yadda kuma tattalin arzikinmu ma yake fuskantar matsin lamba kana yake cikin tsaka mai wuya. Don haka sai ta kirayi 'yan siyasar da su yi abin da ya kamata wajen 'yanto kasar daga cikin irin wannan yanayi da take ciki.

A shekaran jiya ne kotun kolin kasar ta bukaci hukumar zaben kasar da ta dakatar da gudanar da zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka shirya gudanarwa a jiya Talata tana mai cewa wajibi ne a gudanar da bincike da sauraren karar da aka shigar ana zargin gudanar da magudi a zagaye na farko na zaben kafin a gudanar da zagaye na biyun.

Shugaban jam'iyyar Liberty Party (LP) Charles Walker Brumskine ta kasar, wanda kuma shi ne ya zo na uku a zagayen farko na zaben, shi ne ya shigar da karar yana zargin an tafka magudi a yayin zaben.

A da dai an tsayar  za a gudanar da zagaye na biyu na zaben tsakanin tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar George Weah wanda ya zo na daya da mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai wanda ya zo na biyu.