Rahotanni: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 11 A Jihar Flato, Nijeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25373-rahotanni_'yan_bindiga_sun_kashe_mutane_11_a_jihar_flato_nijeriya
Rahotanni daga jihar Filato da ke yankin arewa ta tsakiya a Nijeriya sun bayyana cewar wasu 'yan bindiga dadi sun harbe wasu mutane 11 har lahira a kusa da garin Rim da ke karamar hukumar Riyom da ke jihar, a wani abu da ake gani a matsayin ci gaba da rikicin da wasu suke kokarin sake kunnawa a jihar.
(last modified 2018-08-22T07:00:57+00:00 )
Nov 08, 2017 07:51 UTC
  • Rahotanni: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 11 A Jihar Flato, Nijeriya

Rahotanni daga jihar Filato da ke yankin arewa ta tsakiya a Nijeriya sun bayyana cewar wasu 'yan bindiga dadi sun harbe wasu mutane 11 har lahira a kusa da garin Rim da ke karamar hukumar Riyom da ke jihar, a wani abu da ake gani a matsayin ci gaba da rikicin da wasu suke kokarin sake kunnawa a jihar.

Kafar watsa labaran Premium Times ta Nijeriyar ta ce kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato din Terna Tyopev ya shaida mata cewa lamarin ya faru ne a yammacin jiya Talata a lokacin da mutanen da aka kashe din suke dawowa daga cin kasuwar garin Makera, inda maharan suka kai musu hari; da kashe mutane 11 da kuma raunana wasu hudu na daban. Kakakin ya kara da cewa har ya zuwa yanzu dai ba su kama kowa ba amma dai suna ci gaba da bincike.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin ko kuma bayyana manufar yin hakan.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da wannan harin da kuma kokarin sake haifar da rikici a jihar Filaton yana mai kiran jami'an tsaron kasar da su dau matakan da suka  dace wajen kare lafiya da dukiyoyin al'ummar jihar.