Iran Da DRC Sun Yi Alkawarin Hadin Kai Kan Harkokin Sadarwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25422-iran_da_drc_sun_yi_alkawarin_hadin_kai_kan_harkokin_sadarwa
Babban Darektan harkokin sadarwa na kasashen waje a ma'aikatar al'adu ta Iran da shugaban kamfanin dilancin labaren Jamhuriyar Demokiradiyar Congo sun yi alkawarin hadin gwiwa akan harkokin sadarwa tsakanin kasashen biyu.
(last modified 2018-08-22T11:30:58+00:00 )
Nov 11, 2017 17:02 UTC
  • Iran Da DRC Sun Yi Alkawarin Hadin Kai Kan Harkokin Sadarwa

Babban Darektan harkokin sadarwa na kasashen waje a ma'aikatar al'adu ta Iran da shugaban kamfanin dilancin labaren Jamhuriyar Demokiradiyar Congo sun yi alkawarin hadin gwiwa akan harkokin sadarwa tsakanin kasashen biyu.

Bnagarorin biyu sun bayyana hakan ne a yayin ganawa ta tsakanin babban Darektan harkokin sadarwa na kasashen waje na kasar ta Iran Mohammad Jafar Safi, da na kamfanin lbaren Congo (ACP ) wato Justin Josey a nan birnin Tehran yau Asabar.

Iran ta ce ta yi maraba sosai da cimma wannan yarjejeniya da hadin gwiwa da kamfanin dilancin labaren IRNA na kasar dana ACP na DRC, tare da fatan hakan zai kara karfafa alaka tsakanin kasashen biyu musamen ta bangaren sadarwa.

A nasa bangare Mista Josey, na DRC ya ce yana nadamar akan yadda manyan kafofin yada labarai na duniya basa fadin hakikanin abubuwan da ke faruwa a kasarsa ta DRC.