Buhari Ya Damu Da Yadda Harkokin Ilmi Suke Tafiya A Tarayyar Nigeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25459-buhari_ya_damu_da_yadda_harkokin_ilmi_suke_tafiya_a_tarayyar_nigeria
Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya bayyana matukar damuwarsa kan irin halinda bangaren ilmi da tarbiyya ta shi a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:59+00:00 )
Nov 14, 2017 08:16 UTC
  • Buhari Ya Damu Da Yadda Harkokin Ilmi Suke Tafiya A Tarayyar Nigeria

Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya bayyana matukar damuwarsa kan irin halinda bangaren ilmi da tarbiyya ta shi a kasar.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Litinin a wata zama na musamman da aka gudanar tare da jami'an gwamnatin da abin ya shafa a fadar shugaban kasar.

Shugaban ya kara da cewa yin watsi da harkokin ilmi wanda gwamnatocin da suka gabata suka yi ya kai ga a halin yanzu yara kimani miliyon 13.2 basa zuwa makaranta. Yawan jahilci ya kara yawa a kasar, makarantu sun lalace har ya kai ga babu kwararrun malaman da zasu karantar a makarantun kasar. 

Buhari ya ce ci gaban ko wace kasa a duniya yana tafiya ne da yawan ilminta, don haka dole ne gwamnati ta yi wani shiri don sauya halin da bangaren ilmi yake ciki a kasar.

Kafin jawabinsa Ministan ilmi Malam Adamu Adamu ya bayyana cewa gwamnatin Buhari tana bukatar naira trillion guda a kowace shekara har na tsawon shekaru kafin ta cika alkawulan da ta yiwa mutanen Nigeria a bangaren ilmi.