An Kashe Musulmi 7 A Kasar Afrika Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25462-an_kashe_musulmi_7_a_kasar_afrika_ta_tsakiya
Fada tsakanin masulmi da kuma kiristoci a wata unguwa a birnin Bangi babban birnin kasar afrika ta tsakiya ya lashe rayukana musulmi akalla 7.
(last modified 2018-08-22T07:00:59+00:00 )
Nov 14, 2017 08:19 UTC
  • An Kashe Musulmi 7 A Kasar Afrika Ta Tsakiya

Fada tsakanin masulmi da kuma kiristoci a wata unguwa a birnin Bangi babban birnin kasar afrika ta tsakiya ya lashe rayukana musulmi akalla 7.

Shafin yanar gizi na Al-jazee net ya bayyana cewa da farko wasu mahaya babura sun jefa girneti a cikin wani shagon shan koffi a unguwan da musulmi suka fi yawa a birnin, sannan daga baya suka bude wuta kan wani bikin da ake yi a unguwar wanda ya kai ga mutuwar musulmi 7 da kuma raunata wasu. 

Majiyar kungiyar Seleke ta musulmi ta tabbatar da wannan labarin haka ma majiyar sojojin  tabbatar da zaman lafiya na MDD a cikin birnin ta ce hakan ya faru kuma ana zaton kungiyar anti balaka ta kiristoci a cikin birnin ne suka kai hare haren na jiya Litinin.