Marocco Na Kokarin Yiwa Saudiya Tawaye A Game Da Kasar Qatar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25466-marocco_na_kokarin_yiwa_saudiya_tawaye_a_game_da_kasar_qatar
Sarki kasar Marocco ya kai ziyara birnin Doha, da hakan ke nuna cewa ya karya takunkumin da saudiya ta bukaci kasashen na larabawa suka kakabawa kasar ta Qatar.
(last modified 2018-08-22T07:00:59+00:00 )
Nov 14, 2017 15:29 UTC
  • Marocco Na Kokarin Yiwa Saudiya Tawaye A Game Da Kasar Qatar

Sarki kasar Marocco ya kai ziyara birnin Doha, da hakan ke nuna cewa ya karya takunkumin da saudiya ta bukaci kasashen na larabawa suka kakabawa kasar ta Qatar.

Jaridar Ra'ayil yau ta habarta cewa kasar Marocco na cikin halin daukin mataki na 'yantuwa daga siyasar saudiya a game da kasar Qatar, saboda ziyarar da sarkin kasar Qatar Muhamadu na shida ya kai birnin Doha na nufin karya takunkumin da hukumomin saudiya suka kakabawa kasar ta Qatar

A nata bangare jaridar Sabahul-yau ta kasar Marocco ta rubuta cewa magabatan kasar sun nuna adawa da bukatar saudiya na bayar da rahoto game da ajiyar attajirai da 'ya'yan gidan sarautar ta saudiya  da dan masarautar saudiyar ta tsare kan zarkin su da rashawa.

Babban Attajirin nan kuma dan gidan masarautar saudiya ya zuba hanun jari mai yawa a bankunan kasar ta Marocco sannan kuma yanada kamfanoni da dama a kasar