Kenya: An Kashe 'Yan Hamayyar Siyasa 5 A Yau Juma'a
Nov 17, 2017 18:56 UTC
"Yan sandan kasar ta Kenya sun ce 'yan daba ne suka kashe magoya bayan jagoran adawa Reila Odinga.
Kamfanin dillancin labarun Reuters da ya ambato labarin ya ce 'yan sandan sun ce magoya bayan jagoran adawar Reila Odinga sun yi taro ne ba tare da izini ba, domin tarbarsa a filin saukar jiragen sama bayan tafiyar da ya yi zuwa waje.
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya dauki hotunan gawawwakin mutane biyu da aka kashe su da bindiga a yayin rikicin.
Jami'an tsaron sun yi yi kokarin raba tsakanin masu rikicin, ta hanyar amfani da hayaki da mai sa hawaye.
Tags