Somaliya: An Kame 'Yan Ta'addar Kungiyar al-Shabab 20
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25512-somaliya_an_kame_'yan_ta'addar_kungiyar_al_shabab_20
Gwamnatin kasar Somaliya ce ta sanar da kame 'yan kungiyar ta al-shabab a yankin Shibli.
(last modified 2018-08-22T07:01:00+00:00 )
Nov 17, 2017 15:32 UTC
  • Somaliya: An Kame 'Yan Ta'addar Kungiyar al-Shabab 20

Gwamnatin kasar Somaliya ce ta sanar da kame 'yan kungiyar ta al-shabab a yankin Shibli.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ce; an kame mutanan ne a wani farmaki da jami'an tsaron suka kai a garin na Shibli safli

Majiyar gwamnatin kasar ta Somaliya ta ce; Mutanen da aka kama suna da hanu a wani harin ta'addanci da aka kai a makon da ya gabata, kuma ba da jimawa ba za a gurfantar da su a gaban kotu.

Tun bayan harin da aka kai a cikin watan Oktoba a birnin Magadishu  wanda ya ci rayukan fiye da mutane 350, jami'an tsaron kasar sun fitar da hotunan wasu daga cikin wadanda aka kama din a yanzu.