Zimbabwe: Jam'iyya Mai Mulki Ta Bukaci Shugaba Mugabe Da Ya Yi Murabus
Shugabanin jam'iyar Zanu-PF mai mulki a kasar Zimbabwe ta bukaci shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus daga kan kan mukaminsa.
Tashar telbijin din CNN ta nakalto jam'iyar Zanu-PF mai mulki a kasar ta Zimbabwe a jiya juma'a na cewa ya zama wajibi shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus daga kan kan mukaminsa, dukkunani wakilan jam'iyar na cikin jahohin kasar sun nuna goyon bayansu da wannan mataki da uwar jam'iyar ta zanu-PF ta dauka.
A yau ne kuma ake sa ran za a gudanar da zanga-zanga a birnin Harare domin neman shugaba Mugabe yayi murabus daga kan mukaminsa.
A ranar Larabar da ta gabata ce, rundunar sojin kasar Zimbabwe ta sanar da tsare shugaba mugabe da iyalansa a gida, tare da nemansa ya sauka daga kan karagar mulkin kasar, wannan mataki da rundunar sojin ta dauka na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shugaba Robert Mugabe mai shekaru 93 a duniya ya sauke mataimakinsa Emmerson Mnangagwa domin maye gurbinsa da mai dakinsa Grace Mugabe.