Sojojin Kasar Kenya Sun Halaka Wasu Mayakan Kungiyar Al-Shabab Ta Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2554-sojojin_kasar_kenya_sun_halaka_wasu_mayakan_kungiyar_al_shabab_ta_somaliya
Sojojin gwamnatin Kenya da suke aiki karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somaliya sun kashe wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab a yankin kudancin kasar ta Somaliya.
(last modified 2018-08-22T06:57:59+00:00 )
Mar 17, 2016 02:12 UTC
  • Sojojin Kasar Kenya Sun Halaka Wasu Mayakan Kungiyar Al-Shabab Ta Somaliya

Sojojin gwamnatin Kenya da suke aiki karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somaliya sun kashe wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab a yankin kudancin kasar ta Somaliya.

Kakakin rundunar sojin Kenya a cikin daren jiya Laraba ya fitar da sanarwar cewa: Sojojin gwamnatin Kenya da suke aiki karkashin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika na "AMISON" a kasar Somaliya sun yi wani dauki ba dadi da mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab da suka yi kokarin kutsawa cikin sansanin dakarun kungiyar tarayyar Afrika a yankin yankin kudancin Somaliya, inda gumurzun ya yi sanadiyyar halakar 'yan ta'adda akalla goma sha tara.

Kakakin rundunar sojin ta Kenya ya kara da cewa; Sojojin Kenya sun yi nasarar kwasar ganimar tarin makamai da 'yan ta'addan suka zo da su da nufin yin amfani da su a kan dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar ta tarayyar Afrika.