Daliban Jami'ar Zimbabwe Sun Yi Zanga-Zangar Kin Jinin Mugabe
Daliban jami'ar kasar zimbabwe sun gudanar da zanga-zanga ta neman shugaba Robert Mugabe ya sauka daga kan karagar milki.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a safiyar wannan litinin, daliban jami'ar birnin harare fadar milkin kasar zimbabwe sun gudanar da zanga-zangar neman shugaba Mugabe mai shekaru 93 a duniya ya sauka daga kan kan karagar milkin kasar.
A nasu bangare, shugabanin jami'ar ta birnin Harare sun sanar da dage duk wata jarabbawa da ya kamata daliban suke zana a yau din, har zuwa wani lokaci na daban.
A ranar 15 ga watan Nuwamba ne, dakarun tsaron kasar Zimbabwe suka tsare shugaba Mugabe da iyalansa a gidansa, hakan kuwa ya biyo bayan wata dambarwar siyasa da ta sanya shugaba Mugabe ya sauke mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga kan mikaminsa.
A daren jiya Lahadi ne aka sa rai shugaban zai sanar da murabus a jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin kasar, to amma sai aka samu akasain haka.
A jiya Lahadi Jam’iyyar mai mulki a Zimbabwe, ZANU- PF ta kori Robert Mugabe daga shugabancinta, tare da maye gurbinsa da mataimakinsa da ya kora Emmerson Mnangagwa.