Mayakan Boko Haram Sun Kashe Manoma 6 A Jihar Borno
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25589-mayakan_boko_haram_sun_kashe_manoma_6_a_jihar_borno
Mayakan kungiyar bok oharam sun yi wa wasu manoma shida yankan rago, a kauyen Dimge a kusa da birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.
(last modified 2018-08-22T07:01:01+00:00 )
Nov 20, 2017 15:38 UTC
  • Mayakan Boko Haram Sun Kashe Manoma 6 A Jihar Borno

Mayakan kungiyar bok oharam sun yi wa wasu manoma shida yankan rago, a kauyen Dimge a kusa da birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Rahotanni daga fitowa daga Nigeriya sun tabbatar da cewa wasu mutane  da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe mutane shida ta hanyar yi masu yankan rago, a kauyen Dimge kusa da birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno. Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi,  yayinda manoman ke aiki a gonakinsu.

Maharan na Boko Haram da adadinsu bai fice  bakwai ba sun isa wurin ne a bisa babura inda suka afka wa manoman ne tare da yanka 6 daga cikin su, sannnan kuma  suka kyale wani dattijo don ya kai labari, kamar yadda wani dan kato-da-gora ya tabbatar. Wannan hari ya tayar da hankulan manoma da suka kauracewa gonakinsu, kamar yadda 'yan uwan wadanda aka yanka suka bayyana.

Har ya zuwa yanzu gwamnati da kuma bangaren jami'an tsaro ba su ce uffan ba dangane da wannan hari.