Tarzomar Jama'a Ta Yi Sanadiyyar Jikkata Mutane A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
(last modified Wed, 22 Nov 2017 07:00:27 GMT )
Nov 22, 2017 07:00 UTC
  • Tarzomar Jama'a Ta Yi Sanadiyyar Jikkata Mutane A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

Dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da al'ummar garin Beni da ke lardin Kivu ta Arewa ya yi sanadiyyar jikkatan mutane akalla bakwai.

Al'ummar garin Beni da ke lardin Kivu ta Arewa a shiyar gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da kisan wani matashi da sojojin gwamnatin kasar suka yi lamarin da ya rikide zuwa tarzoma da ta yi sanadiyyar jikkatan mutane akalla bakwai.

Rahotonni sun bayyana cewa: Tarzomar ta yi sanadiyyar jikkatan sojoji biyu da wasu 'yan sanda biyu gami da fararen hula uku kuma daya daga cikinsu mace ce.

Wani jami'i a kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya ce: Matashin da sojojin gwamnatin kasar suka kashe bisa ganganci, shi ne mutum na hudu da sojojin suka kashe a cikin wata guda kacal a garin na Beni da ke lardin Kivu ta Arewa a shiyar gabashin kasar lamarin da ya fusata jama'a suka fito zanga-zangar yin Allah wadai da irin wannan kisa ta wuce gona da iri.