Emmerson Mnangagwa: Zimbabwe Za Ta Hau Turbar Demokradiyya
Wanda zai gaji Robert Mugabe a shugabancin kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da zai saba layar kama aiki a ranar juma'a mai zuwa ya ce; Kasar za ta kama hanyar shimfida sabuwar demokradiyya
Emmerson Mnangagwa, ya kira yi al'ummar kasar da su bai wa gwamnati hadin kai domin tabbatar da demokradiyya a cikin kasar.
Har ila yau Emmerson Mnangagwa ya jinjinawa sojojin kasar saboda hikimar da suka yi amfani da ita ba tare da amfani da tashin hankali ba.
Al'ummar kasar ta Zimbabwe suna nuna damuwarsu akan wanda zai gaji Mugane saboda mummunar rawar da ya taka a lokacin da ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa.
Ita ma kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International ta nuna damuwa akan halin kama-karya na Emmerson Mnangagwa a tsawon lokacin da yake mataimakin shugaban Mugabe.