Emmerson Mnangagwa: Zimbabwe Za Ta Hau Turbar Demokradiyya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25661-emmerson_mnangagwa_zimbabwe_za_ta_hau_turbar_demokradiyya
Wanda zai gaji Robert Mugabe a shugabancin kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da zai saba layar kama aiki a ranar juma'a mai zuwa ya ce; Kasar za ta kama hanyar shimfida sabuwar demokradiyya
(last modified 2018-08-22T11:31:02+00:00 )
Nov 23, 2017 06:30 UTC
  • Emmerson Mnangagwa: Zimbabwe Za Ta Hau Turbar Demokradiyya

Wanda zai gaji Robert Mugabe a shugabancin kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da zai saba layar kama aiki a ranar juma'a mai zuwa ya ce; Kasar za ta kama hanyar shimfida sabuwar demokradiyya

Emmerson Mnangagwa, ya kira yi al'ummar kasar da su bai wa gwamnati hadin kai domin tabbatar da demokradiyya a cikin kasar.

Har ila yau Emmerson Mnangagwa ya jinjinawa sojojin kasar saboda hikimar da suka yi amfani da ita ba tare da amfani da tashin hankali ba.

Al'ummar kasar ta Zimbabwe suna nuna damuwarsu akan wanda zai gaji Mugane saboda mummunar rawar da ya taka a lokacin da ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa.

Ita ma kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International ta nuna damuwa akan halin kama-karya na Emmerson Mnangagwa a tsawon lokacin da yake mataimakin shugaban Mugabe.