Masar Ta Dage Takunkumin Bayar Da Visa Ga 'Yan Kasar Qatar
(last modified Thu, 23 Nov 2017 11:45:28 GMT )
Nov 23, 2017 11:45 UTC
  • Masar Ta Dage Takunkumin Bayar Da Visa Ga 'Yan Kasar Qatar

Ministan cikin gidan kasar Masar ya bayar da umarnin dage takunkumin bayar da visar gaggauwa ga 'yan kasar Qatar.

A jiya laraba ministan cikin gidan kasar Masar Magdi Abdel-Ghaffar ya sanya hannu a cikin wata sabuwar doka da ta bayar da damar dage takunkumin bayar da visar gaggauwa ga 'yan kasar Qatar.

A tsakiyar watan oktoban da ya gabata ne, kasar ta Masar ta dauki kudirin hana 'yan kasar Qatar visar gaggauwa wacce ake bayarwa a filin jirgi, hakan kuwa ya biyo bayan goyon bayan da kasar Masar ta baiwa kasashen saudiya, hadaddiyar daular larabawa, da Bahren na yanke alakar diplomasiya da kasar ta Qatar, bayan da suka zarke ta da taimakawa 'yan ta'adda.

Ko baya ga wannan, tun a watan yunin 2013, alaka tsakanin kasashen Masar da Qatar ta tabarbare bayan juyin milkin da aka yi wa zababen shugaban kasar ta Masar Muhamad Mursi.