Zimbabwe : Mugabe Zai Halarci Bikin Rantsar Da Mnangagwa
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, zai halarci bikin rantsar da tsohon mataimakin Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar.
A gobe JUma'a ne aake rantsar da Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasar, inda kuma ake sa ran Mugabe zai halarci bikin, kamar yadda gidan talabijin din kasar na ZBC ya sanar.
A yanzu haka dai komi ya kankama a shirye-shiryen ranatsar da Mnangagwa a bikin da za'a gudanar a filin kwallon kafa na kasar dake Harare fadar mulkin kasar ta Zimbabwe.
Shugaba mai barin gado Mugabe zai gana da sojojin kasar a cikin tsarin yi masu ban kwana a yayin da shu kuwa sabon shugaban kasar zai shiga faretin sojojin.
A ranar 6 ga watan Nuwamba nan ne, shugaba Mugabe ya kori mataimakinsa a daidai lokacin aka shiga takun tsaka tsakaninsa da uwal gidan Mugabe cewa da Grace wacce suke jayayar neman gajiyar iko daga Mugabe mai shekaru 93, lamarin da ya kai ga sojoji suka tunkube daga madafun iko, suyka kuma mas adarmun talala na tsawon 'yan kwanaki kafin daga bisani ya aike da wasikar yin murabus daga shugabancin kasar bayan shafe shekaru 37 kan karagar mulki.