Bauta A Libiya : Ruwanda Za Ta Karbi Bakin Haure 30,000
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25713-bauta_a_libiya_ruwanda_za_ta_karbi_bakin_haure_30_000
Kasar Ruwanda ta ce a shirye ta ke ta karbi bakin haure 'yan Afrika har zuwa 30,000 dake cikin halin kunci a kasar Libiya, inda aka bankado labarin cinikin bakin haure tamakar bayi a kasar ta Libiya.
(last modified 2018-08-22T07:01:02+00:00 )
Nov 23, 2017 14:31 UTC
  • Bauta A Libiya : Ruwanda Za Ta Karbi Bakin Haure 30,000

Kasar Ruwanda ta ce a shirye ta ke ta karbi bakin haure 'yan Afrika har zuwa 30,000 dake cikin halin kunci a kasar Libiya, inda aka bankado labarin cinikin bakin haure tamakar bayi a kasar ta Libiya.

Batun cinikin bakin haure tamakar bayi a kasar Libiya da aka tashar talabijin ta CNN ta fitar a wani rahoto na ci gaba da shan suka da tsofin Allah tsine daga shuwagabanni da kungiyoyin musamen na Afrika a baya bayan nan.

Ruwanda ta ce yanzu haka tana kan tattaunawa na ganin ya zata yi na taimakawa ta hanyar karbar bakin hauren fursunini a kasar ta Libiya, kamar yadda ministar harkokin wajen kasar Mme Louise Mushikiwabo ta sanar.

Mme Mushikiwabo ta ce abun takaici ne yadda ake tsare maza da mata da yara dake kan hanyarsu ta zuwa turai ana bautar da su.

Ita ma faransa a watasa sanarwa data fitar a jiya ta bukaci wani taron gaggawa na kwamitin tsaron  MDD kan batun na cinikin bakin haure a Libiya ta nuna taklaici akan lamarin data daganta da cin zarafin bil adama.