Zimbabwe : An Ba Wa Mugabe Rigar Kariya
(last modified Fri, 24 Nov 2017 05:14:46 GMT )
Nov 24, 2017 05:14 UTC
  • Zimbabwe : An Ba Wa Mugabe Rigar Kariya

Wata majiya ta bayyana cewar an ba wa tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe kariya da za ta hana shi fuskantar shari'a tare kuma da tabbatar da tsaronsa a cikin kasar lamarin da ya sanya shi yarda yayi murabus daga karagar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wata majiya ta kurkusa da tattaunawar da ta gudana kafin yin murabus din Mugaben tana cewa Mugaben ya shaida wa masu tattaunawar cewa yana fatan mutuwa a kasar Zimbabwen ba a wata kasa ta daban ba, don haka aka ba shi lamunin tabbatar da tsaronsa a kasar da kuma ba shi rigar kariya daga yin masa shari'a.

A ranar Talatar da ta gabata ce shugaba Mugabe dan shekaru 93 a duniya ya sanar da saukarsa daga kujerar mulkin kasar wanda ya shafe shekaru 37 yana kai don lokacin da kasar ta sami 'yancin kanta daga Birtaniyya a  shekarar 1980. A makon da ya wuce ne dai sojojin kasar suka kwace madafun ikon kasar da sanya Mugaben karkashin daurin talala wanda hakan ne ya share fagen yin murabus din nasa.

A yau Juma'a ce ake sa ran rantsar da Emmerson Mnangagwa, tsohon mataimakin shugaban kasar wanda Mugaben ya kora daga mulki  a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe na wucin gadi don  karasa wa'adin mulkin Mugaben har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a shekara mai kamawa.