Lai Muhammad: Fitinar Kirkiro Biafra Na Kungiyar IPOB Ya Kawo Karshe
Ministan watsa labaru da al'adu na Nijeriya Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewar fitinar kirkiro kasar Biafra da kungiyar 'yan aware ta Inyamurai IPOB ta tayar ya kawo karshe yana mai cewa kungiyar ba ta da wani goyon baya mai karfi a yankin Kudu maso yammacin kasar.
Kafar watsa labaran Africanews ta bayyana cewar Alhaji Lai Muhammad ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriyan inda ya ce fitowar da al'ummar jihar Anambra suka yi yayin zaben gwamna da aka gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Nuwamban nan duk da kiraye-kirayen da kungiyar IPOB din ta yi na a kaurace wa zaben wata alama ce da ta ke nuni da karshe da mutuwar kungiyar ta IPOB.
Alhaji Lai Muhammad ya ci gaba da cewa yin watsi da kiran kaurace wa zaben da al'ummar jihar Anambran suka yi na nuni da cewa kungiyar ta IPOB ba ta wakiltan al'ummar jihar da ma sauran jihohin Kudu maso gabashin Nijeriyan.
Kungiyar IPOB din dai ta kirayi al'ummar jihar Anambran da su kaurace wa zaben da kuma sha alwashin hana shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari zuwa jihar, to sai dai kuma shugaba Buharin ya je jihar sannan kuma an gudanar da zaben lami lafiya.