An Rantsar Da Sabon Shugaban Zimbabwe
A yau Juma'a ne aka rantsar da Emmerson Mnangagwa mataimakin shugaba Robert Mugabe a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe kuma shugaban kasar na uku a kasar tun bayan samun yancin kai a shekara ta 1980.
Bayan rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe a gaban dubban al'ummar Zimbabwe a babban filin wasanni na birnin Harare a yau Juma'a: Emmerson Mnangagwa dan shekaru 75 a duniya kuma tsohon mataimakin shugaba Ribert Mugabe ya daga murya yana mai shelanta wa al'ummar kasar cewa: A shekara mai kamawa ta 2018 za a gudanar da zabuka cikin 'yanci da walwala a kasar Zimbabwe, kuma al'ummar kasar zasu zabar wa kansu shugabanni.
Sabon Shugaban kasar ya bayyana cewa: Dole ne mu yi furuci da irin gagarumar rawar da shugaban Robert Mugabe mai ritaya ya taka a fagen ci gaban kasar Zimbabwe musamman gwagwarmayar kwato 'yancin kasar daga hannun turawan mulkin mallaka.
Yau kimanin makonni uku ke nan da suka gabata shugaba Robert Mugabe ya kori mataimakinsa kuma babban jami'in leken asirin kasar Emmerson Mnangagwa daga kan mukaminsa a kokarin da yake yi na nada matarsa a matsayin wadda zata gaje shi lamarin da ya sanya sojojin kasar suka karbe iko da kasar ta Zimbabwe tare da kame manyan jami'an gwamnatin Mugabe, kuma al'ummar Zimbabwe da jam'iyya mai mulki a kasar ta Zanu-PF tsuka bukaci Robert Mugabe da yayi murabus daga kan karagar shugabancin kasar bayan shafe tsawon shekaru 37 yana mulki.