Rikici Ya Sake Barkewa A Afirka Ta Kudu
(last modified Sun, 26 Nov 2017 12:13:12 GMT )
Nov 26, 2017 12:13 UTC
  • Rikici Ya Sake Barkewa A Afirka Ta Kudu

Wata majiya ta ce an fara fada mai tsanani tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a jumhoriyar Afirka ta tsakiya.

Kamfanin dillancin Xin huwa na kasar China ya nakalto wata majiya daga birnin Bangui na cewa wani sabon fada ya sake barkewa tsakanin tsohuwar kungiyar 'yan tawayen saleka karkashin komanda Abdullahi Haisan da wata kungiya mai dauke da makamai a arewa da yammancin jumhoriyar Afirka ta tsakiya.

Majiyar ta ce rikicin yayi tsakani a arewa da yammacin kasar, kuma saboda tsananin tsoro, mazauna yankin sun yi hijra zuwa sansanin 'yan gudun hijra  dake kusa da sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

Har ila yau majiyar ta ce ana fuskantar karamcin abinci a yankunan da fadan ya barke kuma kungiyoyin kai agaji na  kasa da kasa sun kasa magance matsalar al'ummar yankin.