Sudan: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Sojoji Hari A Yankin Darfur.
Nov 27, 2017 08:23 UTC
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa 'yan bindigar sun kashe sojojin Sudan 10 a yankin Darfur ta yamma
An kai harin ne dai a lokacin da sojojin gwamnatin kasar ta Sudan suke kokarin karbar makamai daga mutane yankin da ya yi fama da fadace-fadace.
Gwamnatin kasar ta Sudan ta fito da shirin kwance damarar mutanen yakin na Darfur ta hanyar yin kira a gare su da su mika makaman nasu bisa radin kansu, domin samun tukuicin kudade.
Tun a 2003 ne yankin na Darfur ya fada cikin yaki da gwmanatin Khartum, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan da suka kai 300,000 da kuma mayar da wasu miliyan biyu da 500,000 'yan gudun hijira.
Tags