An Kafa Wata Sabuwar Kungiyar Yan Tawaye A Kasar Sudan Ta Kudu
(last modified Mon, 27 Nov 2017 19:01:31 GMT )
Nov 27, 2017 19:01 UTC
  • An Kafa Wata Sabuwar Kungiyar Yan Tawaye A Kasar Sudan Ta Kudu

Wani komandan sojojin kasar Sudan ta Kudu mai suna Zakariyya Munjik faqut ya bayyana ballewarsa daga sojojin gwamnati da kuma kafa wata sabuwar kungiyar yan tawaye don kubutar da kasar daga hannun shugaba Silva Kirr.

Kamfanin dillancin labaran Anatolio ya nakalto Zakariyya munjik yana fadar haka a yau Litinin, ya kuma kara da cewa sunan kungiyarsa ita ce -hadaddiyar kungiyar kwatoto 'yencin kudancin sudan-. Zakariyya ya bayyana cewa a halin yanzu shi da sojojinsa sun yi sansani a yankin arewa maso yammacin kasar kan iyaka da kasar Sudan.

Jami'in sojan  yana zirgin shugaba Silva kirr da samar da yakin kabilanci a kasar sudan ta kudu, sannan ya ci zai ci gaba da yakarsa har sai ya sauka don a gudanar da zabe cikin adalci.

Kafin haka dai kasar sudan ta kudu tana da kungiyoyin yan tawaye har 6 wadanda suka fafatawa da sojojin shugaba silva kirr.